ZAB 129

Addu’a a kan Maƙiyan Isra’ila

1 Isra’ila, sai ka faɗi irin muguntar

Da maƙiyanka suka tsananta maka da ita,

Tun kana ƙarami!

2 “Maƙiyana suka tsananta mini da mugunta,

Tun ina ƙarami,

Amma ba su yi nasara da ni ba.

3 Suka sa mini raunuka masu zurfi a bayana,

Suka mai da shi kamar gonar da aka nome.

4 Amma Ubangiji mai adalci,

Ya ‘yantar da ni daga bauta.”

5 Allah ya sa duk waɗanda suke ƙin Sihiyona,

A yi nasara da su a kuma kore su!

6 Allah ya sa su zama kamar ciyawar da take girma a kan soraye,

Ta kuwa bushe kafin ta isa yanka.

7 Ba wanda zai tattara ta,

Ya ɗaure ta dami dami.

8 Duk waɗanda suke wucewa a hanya ba za su ce,

“Ubangiji ya sa maka albarka!” ba,

Ko su ce, “Muna sa maka albarka da sunan Ubangiji!”