ZAB 130

Sa Zuciya ga Ceton Allah

1 A cikin fid da zuciyata,

Na yi kira gare ka, ya Ubangiji.

2 Ka ji kukana, ya Ubangiji,

Ka kasa kunne ga kiran da nake yi na neman taimako!

3 Idan kana yin lissafin zunubanmu,

Wa zai kuɓuta daga hukunci?

4 Amma kakan gafarta mana,

Domin mu zama masu tsoronka.

5 Na zaƙu, ina jiran taimako daga Ubangiji,

Ga maganarsa na dogara.

6 Ina jiran Ubangiji,

Na zaƙu ƙwarai, fiye da matsara waɗanda suke jiran ketowar alfijir,

I, fiye da matsara waɗanda suke jiran ketowar alfijir.

7 Ya Isra’ila, ki dogara ga Ubangiji,

Saboda ƙaunarsa madawwamiya ce,

A koyaushe yana da nufin yin gafara.

8 Zai fanshi jama’arsa Isra’ila

Daga dukan zunubansu.