ZAB 132

Yabo saboda Tsattsarkan Wuri

1 Ya Ubangiji, kada ka manta da Dawuda

Da dukan irin aikin da ya yi.

2 Ka tuna, ya Ubangiji, da alkawarin da ya yi,

Da rantsuwar da ya yi maka, ya Maɗaukaki, Allah na Isra’ila,

3 “Ba zan tafi gida ko in kwanta ba,

4 Ba zan huta, ko in yi barci ba,

5 Sai sa’ad da na shirya wa Ubangiji wuri,

Wato Haikali domin Maɗaukaki, Allah na Isra’ila.”

6 Mun ji labari akwatin alkawari yana Baitalami,

Amma muka same shi a kurmi.

7 Muka ce, “Bari mu tafi Haikalin Ubangiji,

Mu yi sujada a gaban kursiyinsa!”

8 Ka zo wurin hutawarka, ya Ubangiji,

Tare da akwatin alkawari,

Alama ce ta ikonka.

9 Ka suturta firistoci da adalci,

Ka sa dukan jama’arka su yi sowa ta farin ciki!

10 Ka yi wa bawanka Dawuda alkawari,

Kada ka rabu da zaɓaɓɓen sarkinka, ya Ubangiji!

11 Ka yi wa Dawuda muhimmin alkawari,

Ba kuwa za ka ta da alkawarin ba.

Ka ce, “Za naɗa ɗaya daga cikin ‘ya’yanka maza yă zama sarki,

Zai yi mulki a bayanka.

12 Idan ‘ya’yanka maza za su amince da alkawarina,

Da umarnan da na yi musu,

‘Ya’yansu maza kuma za su bi bayanka su zama sarakuna,

A dukan lokaci.”

13 Ubangiji ya yaɓi Sihiyona,

A can yake so ya gina Haikalinsa, ya ce,

14 “A nan zan zauna har abada.

A nan kuma nake so in yi mulki.

15 Zan tanada wa Sihiyona dukan abin da take bukata a yalwace,

Zan ƙosar da matalautanta da abinci.

16 Zan sa firistocinta su yi shela,

Cewa ina yin ceto,

Jama’ata kuma za su raira waƙa,

Suna sowa don farin ciki.

17 A nan ne zan naɗa ɗaya daga cikin zuriyar Dawuda

Yake zama babban sarki,

A nan ne kuma zan wanzar da

Mulkin zaɓaɓɓen sarkina.

18 Zan sa maƙiyansa su sha kunya,

Amma mulkinsa zai arzuta.

Ya kuma kahu.”