ZAB 135

Waƙar Yabon Girman Ubangiji

1 Ku yabi Ubangiji!

Ku yabi sunansa, ku bayin Ubangiji,

2 Ku da kuke tsaye a Haikalin Ubangiji,

A wuri mai tsarki na Allahnmu.

3 Ku yabi Ubangiji, domin nagari ne shi,

Ku raira yabbai ga sunansa, domin shi mai alheri ne.

4 Ya zaɓar wa kansa Yakubu,

Jama’ar Isra’ila kuwa tasa ce.

5 Na sani Ubangijinmu mai girma ne,

Ya fi dukan alloli girma.

6 Yana aikata dukan abin da ya ga dama a Sama ko a duniya,

A tekuna, da kuma zurfafan da suke ƙarƙas.

7 Yakan kawo gizagizan hadiri daga bangayen duniya,

Yakan yi walƙiya domin hadura,

Yakan fito da iska daga cikin taskarsa.

8 A Masar ne ya karkashe ‘ya’yan fari na mutane da na dabbobi.

9 A can ne ya aikata mu’ujizai da al’ajabai,

Domin ya hukunta Fir’auna da dukan hukumar ƙasarsa.

10 Ya hallakar da sauran al’umma masu yawa,

Ya karkashe sarakuna masu iko, wato

11 Sihon, Sarkin Amoriyawa, da Og, Sarkin Bashan,

Da dukan sarakunan Kan’ana.

12 Ya ba da ƙasarsu ga jama’arsa,

Ya ba da ita ga Isra’ila.

13 Ya Ubangiji, kullayaumi mutane za su sani kai ne Allah,

Dukan tsararraki za su tuna da kai.

14 Ubangiji zai ji juyayin mutanensa,

Zai ‘yantar da bayinsa.

15 Gumakan al’ummai, da azurfa da zinariya aka yi su,

Hannuwan mutane ne suka siffata su.

16 Suna da bakuna, amma ba sa magana,

Da idanu, amma ba sa gani.

17 Suna da kunnuwa, amma ba sa ji,

Ba kuma numfashi a bakinsu.

18 Ka sa su waɗanda suka yi su,

Da dukan waɗanda suke dogara gare su,

Su zama kamar gumakan da suka yi!

19 Ku yabi Ubangiji, ya jama’ar Isra’ila,

Ku yabe shi, ya ku firistocin Allah!

20 Ku yabi Ubangiji, ya ku Lawiyawa,

Ku yabe shi, dukanku da kuke tsoronsa!

21 Ku yabi Ubangiji a Sihiyona da a Urushalima, wato a Haikalinsa.

Ku yabi Ubangiji!