ZAB 137

Kukan Isra’ilawa a Baƙuwar Ƙasa

1 A bakin kogunan Babila

Muka zauna muka yi ta kuka,

Sa’ad da muka tuna da Sihiyona.

2 A rassan itatuwan wardi da suke kusa da mu

Muka rataye garayunmu.

3 Waɗanda suka kama mu suka sa mu mu yi waƙa,

Suka ce mana, “Ku yi mana shagali

Da waƙar da aka raira wa Sihiyona!”

4 Kaƙa za mu raira waƙar Ubangiji

A baƙuwar ƙasa?

5 Da ma kada in ƙara iya kaɗa garaya,

Idan na manta da ke, Urushalima!

6 Da ma kada in ƙara iya raira waƙa,

Idan na manta da ke,

Idan ban tuna ke ce

Babbar abar farin ciki ba!

7 Ka tuna, ya Ubangiji, da abin da Edomawa suka yi,

A ranar da aka ci Urushalima.

Ka tuna da yadda suka ce,

“A ragargaza ta har ƙasa!”

8 Babila, za a hallaka ki!

Mai farin ciki ne shi wanda ya sāka miki

Bisa ga abin da kika yi mana.

9 Mai farin ciki ne shi wanda zai kwashi jariranki

Yă fyaɗa su a kan duwatsu!