ZAB 53

Muguntar Mutane

1 Wawaye sukan ce wa kansu, “Ba Allah.”

Dukansu sun lalace, sun aikata mugayen al’amura,

Ba wanda yake aikata abin da yake daidai.

2 Daga Sama Allah ya dubi mutane,

Ya ga ko akwai masu hikima

Waɗanda suke yi masa sujada.

3 Amma dukansu sun koma baya,

Su duka mugaye ne,

Ba wanda yake aikata abin da yake daidai,

Babu ko ɗaya.

4 Allah ya ce, “Ashe, ba su sani ba?

Ashe, mugayen nan jahilai ne?

Ta wurin yi wa jama’ata fashi suke rayuwa,

Ba sa yin addu’a gare ni.”

5 Amma sa’an nan za su firgita ƙwarai,

Irin yadda ba su taɓa yi ba,

Gama Allah ya warwatsa ƙasusuwan maƙiyanka.

Ya kore su sarai, saboda ya ƙi su.

6 Dā ma ceto ya zo ga Isra’ila daga Sihiyona!

Sa’ad da Allah ya sāke arzuta jama’arsa,

Zuriyar Yakubu za ta yi farin ciki,

Jama’ar Isra’ila kuwa za ta yi murna.