ZAB 54

Addu’ar Neman Tsari daga Maƙiyi

1 Ka cece ni ta wurin ikonka, ya Allah,

Ka cece ni ta wurin ƙarfinka!

2 Ka ji addu’ata, ya Allah,

Ka saurari kalmomina!

3 Masu girmankai sun tasar mini,

Mugaye suna nema su kashe ni,

Mutanen da ba su kula da Allah ba.

4 Na sani Allah ne mai taimakona,

Na sani Ubangiji shi ne mai tsarona!

5 Ubangiji ya hukunta wa maƙiyana da irin muguntarsu!

Gama zai hallaka su saboda shi mai aminci ne.

6 Da murna zan miƙa maka hadaya,

Zan yi maka godiya, ya Ubangiji,

Domin kai mai alheri ne.

7 Ka cece ni daga dukan wahalaina,

Na kuwa ga an kori maƙiyana.