ZAB 55

Addu’ar Neman Taimako

1 Ka ji addu’ata, ya Allah,

Kada ka ƙi jin roƙona!

2 Ka saurare ni, ka amsa mini,

Gama damuwata ta gajiyar da ni tiƙis.

3 Hankalina ya tashi saboda yawan kurarin maƙiyana,

Saboda danniyar mugaye.

Sukan jawo mini wahala,

Suna jin haushina suna ƙina.

4 Azaba ta cika zuciyata,

Tsorace-tsoracen mutuwa sun yi mini nauyi.

5 Tsoro da rawar jiki sun kama ni,

Na cika da razana.

6 Na ce, “Da a ce ina da fikafikai kamar kurciya,

Da sai in tashi, in tafi, in nemi wurin hutawa!

7 In tafi can nesa,

In yi wurin zamana a hamada.

8 Zan hanzarta in nemi mafaka

Daga iska mai ƙarfi da hadiri.”

9 Ka hallaka su, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu,

Gama na ga hargitsi da tawaye a birni.

10 Dare da rana suna ta yawo a kan garu suna ta kewaye birnin,

Birnin kuwa cike yake da laifi da wahala.

11 Akwai hallaka a ko’ina,

Tituna suna cike da azzalumai da ‘yan danfara.

12 Da a ce maƙiyina ne yake mini ba’a,

Da sai in jure.

Da a ce abokin gābana ne yake shugabancina,

Da sai in ɓuya masa.

13 Amma kai ne, aminina,

Abokin aikina ne, abokina ne kuma!

14 Dā mukan yi taɗi da juna ƙwarai,

Mukan tafi Haikali tare da sauran jama’a.

15 Allah ya sa mutuwa ta auko wa maƙiyana ba labari,

Allah ya sa su gangara ƙasar matattu da ransu!

Mugunta tana cikin gidajensu da zukatansu.

16 Amma ina kira ga Allah, yă taimake ni,

Ubangiji kuwa zai cece ni.

17 Koke-kokena da nishe-nishena

Suna hawa zuwa gare shi da safe, da tsakar rana, da dad dare,

Zai kuwa ji muryata.

18 Zai fisshe ni lafiya

Daga yaƙe-yaken da nakan yi da magabtana masu yawa.

19 Allah, shi wanda yake mulki tun fil azal,

Zai ji ni, zai kore su.

Ba abin da suka iya yi a kai,

Domin ba su tsoron Allah.

20 Abokina na dā,

Ya yi wa abokansa faɗa,

Ya ta da alkawarinsa.

21 Kalmominsa sun fi mai taushi,

Amma ƙiyayya tana a zuciyarsa,

Kalmominsa sun fi mai sulɓi,

Amma suna yanka kamar kakkaifan takobi.

22 Ka gabatar da wahalarka ga Ubangiji,

Zai kuwa taimake ka,

Ba zai bari a ci nasara a kan mutumin kirki ba, faufau.

23 Amma kai, ya Allah, za ka jefar da masu kisankai, da maƙaryata can ƙasa cikin zurfafa,

Kafin su kai rabin kwanakinsu a duniya.

Amma ni, zan dogara gare ka.