ZAB 56

Addu’ar Dogara ga Allah

1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah,

Gama mutane sun tasar mini,

Maƙiyana suna tsananta mini koyaushe!

2 Dukan yini maƙiyana suna tasar mini,

Waɗanda suke faɗa da ni sun cika yawa.

3 Sa’ad da nake jin tsoro, ya Maɗaukaki,

A gare ka nake dogara.

4 Ga Allah nake dogara, ina yabon alkawarinsa,

Gare shi na dogara, ba zan ji tsoro ba.

Me mutum kawai zai yi mini?

5 Maƙiyana suke ta wahalshe ni dukan yini,

A kan kowane abu da nake yi,

Kullum suna ta tunanin yadda za su cuce ni!

6 Sukan taru a ɓoye,

Suna kallon duk abin da nake yi.

Suna sa zuciya za su iya kashe ni.

7 Ka hukunta su, ya Allah saboda muguntarsu,

Da fushinka ka kori waɗannan mutane!

8 Ka san irin wahalar da nake sha,

Kana riƙe da lissafin yawan hawayena.

Ashe, ba a rubuce suke a littafinka ba?

9 A ranar da na yi kira gare ka,

Za a komar da abokan gābana baya,

Gama na sani Allah yana tare da ni!

10 Ina dogara ga Allah, ina yabon alkawarinsa,

Ina dogara ga Ubangiji, ina yabon alkawarinsa.

11 A gare shi nake dogara,

Ba zan ji tsoro ba.

Me mutum kawai zai yi mini?

12 Zan miƙa maka abin da na yi alkawari, ya Allah,

Zan miƙa maka hadaya ta godiya.

13 Domin ka cece ni daga mutuwa,

Ka hana a ci nasara a kaina.

Saboda haka a gaban Allah nake tafiya

A hasken da yake haskaka wa masu rai.